Gwamnonin Arewa maso Gabas za su samar da jirgin sama na yankin

WhatsApp Image 2026 10 03 at 9.06.48 PM 750x430

Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF), a ranar Asabar ta fitar da wata takarda mai dauke da kudurori 11 a karshen taronta na yau da kullum karo na 13, wanda ya gudana a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Ɗaya daga cikin matsayun da suka cimma shi ne kafa North-East Air Shuttle, wato kamfanin jigilar jirgin sama na yankin.

Gwamnonin sun sake amincewa baki ɗaya da ci gaba da magana da murya ɗaya da kuma aiki da manufa guda kan batutuwan da suka shafi yankin, musamman tsaro, haɗin kan al’umma, tattalin arziki da ci gaba.

Taron ya gudana karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda shi ne kuma Shugaban NEGF kuma mai masaukin baki.

Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe, da Mataimakin Gwamnan Bauchi, Mohammed Auwal Jatau, wanda ya wakilci gwamnan jihar.

Haka kuma, Mataimakin Gwamnan Yobe, Idi Barde Gubana, ya wakilci Gwamnan Yobe a taron.

Gwamnan Jihar Taraba da mataimakinsa ba su samu halartar taron ba.

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, shi ma yana cikin waɗanda suka halarci taron.

Da yake karanta sanarwar da aka fitar a ƙarshen taron, Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce ƙungiyar na ci gaba da yaba wa irin haɗin kai da haɗin gwiwar da ake samu tsakanin jihohin mambobin ƙungiyar tun bayan taronta na farko da aka gudanar a Gombe a watan Maris na 2020.

Ya ce rawar da ƙungiyar ke takawa har yanzu tana ci gaba da bunƙasa.

Ga wasu daga cikin muhimman matsayoyin da ƙungiyar ta cimma:

Ƙungiyar ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara cikin shekaru shida da suka gabata, inda ta ce muhimmiyar nasarar ita ce haɗin kan gwamnonin ƙungiyar, wanda ya taimaka wajen samun sakamako mai amfani a fannin samar da ayyukan alheri a yankin.

Ƙungiyar ta yaba wa Shugaban Ƙasa kan sabon kulawar da aka bai wa layin dogo na Port Harcourt–Jos–Bauchi–Gombe–Maiduguri, da kuma aikin neman man fetur a Kolmani da kuma hanyar Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe–Biu–Maiduguri.

Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba ayyukan neman man fetur da aka fara a baya amma daga bisani suka tsaya a ƙananan hukumomin Magumeri da Gubio na Jihar Borno.

Gwamnonin sun kuma yaba wa ƙoƙarin jihohi mambobin ƙungiyar wajen samar da wutar lantarki da bunƙasa makamashi a yankin. Sun ce hakan ya mayar da batun makamashi daga matsalar kowace jiha zuwa batun da ya shafi yankin baki ɗaya.

Sun bayyana cewa tashar samar da wutar lantarki ta Dadinkowa yanzu tana samar da wuta zuwa babban layin wutar lantarki na ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here