European American University ta karyata bikin yaye dalibai a Abuja da aka ce ta ba Rarara digiri, ta kira shi na yaudara

WhatsApp Image 2025 09 20 at 17.28.15 1 750x430

European American University (EAU) ta fitar da sanarwa tana nesanta kanta daga wani rahoto na kafafen yada labarai da ya ce ta karrama mawakin siyasa na Hausa, Dauda Kahutu Rarara, da digirin girmamawa a wani biki da aka gudanar a Abuja.

A cikin wata sanarwa da jami’ar ta wallafa a shafinta na Internet a ranar Asabar, ta bayyana cewa taron da aka ce an gudanar a NICON Luxury Hotel, Abuja, an shirya shi ne ba tare da sani ko yardar jami’ar ba, tana mai kiran lamarin a matsayin na yaudara.

Jami’ar ta jaddada cewa ba Rarara ba, ko kuma sauran mutanen da aka ambata a cikin rahotanni ciki har da Alhaji Ahmed Saleh Jnr., Farfesa Mustapha Abdullahi Bujawa, da Farfesa Tarela Boroh sun samu wani digiri na girmamawa daga gare ta.

Ta kuma gargadi al’umma da su yi hattara da irin wadannan shirye-shiryen da ba su da tushe, tana mai cewa jami’ar tana bin sahihan hanyoyin doka da ka’ida wajen bayar da duk wani digiri na girmamawa.

Jami’ar Turai da Amurka ta karyata rawar da ake cewa wasu suna takawa a cikinta, ta ce za ta dauki mataki kan masu buga takardun bogi

Jami’ar (EAU) ta sake jaddada cewa mutanen da ake alakanta da ita a bikin da aka gudanar a Abuja ba su taba samun wata girmamawa daga gare ta ba, kuma ba su da wata halastacciyar alaƙa da jami’ar.

A cewar sanarwar: “Waɗannan mutane ba masu karɓar girmamawa daga jami’ar ba ne, kuma ba su da wata alaka da mu.”

Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa jami’ar ta kuma nesanta kanta daga Musari Audu Isyaku, wanda aka ce wakilinta ne a Arewacin Najeriya, tare da karyata cewa Idris Aliyu na cikin majalisar gudanarwarta.

Karin labari: Rarara ya samu digirin girmamawa

Jami’ar ta fayyace cewa babu irin wannan majalisar gudanarwa a wurinta, sannan ta kara da cewa an soke wa Aliyu mukamin girmamawa da aka ba shi a baya saboda zargin hannu a cikin wannan harkallar bogi.

Haka kuma, jami’ar ta tunatar da jama’a cewa tsohuwar shugabar jami’ar, Dr. Josephine Egbuta, an tsige ta tun farkon shekarar nan, don haka ba ta da ikon wakiltar jami’ar a kowane mataki.

Ta bayyana cewa shugaban jami’ar na yanzu shi ne Farfesa Luca Scotto di Tella de’ Douglas di Castel di Ripa.

Dangane da matsayinta na doka, jami’ar ta bayyana cewa an kafa ta a matsayin cibiyar ilimi mai zaman kanta, kuma tana da takardar izinin sarauta daga Masarautar Bunyoro-Kitara da ke Uganda.

Ta yi watsi da duk wata alaƙa da ake yi mata da Dominica da Panama, tana mai cewa tsohon bayani ne marar inganci.

Sanarwar ta kara da cewa jami’ar za ta hada kai da hukumomin Najeriya domin dakatar da bayar da takardun bogi da sunanta, tare da tabbatar da gurfanar da duk wanda ya yi hannu a ciki a gaban doka.

Haka kuma, ta sanar da cewa bikin karramawarta na gaba a Najeriya zai gudana ne a ranar 15 ga Nuwamba, 2025, sannan wani biki na musamman zai gudana a Malaysia a watan Disamba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here