EAU ta nisanta kanta da digirin girmamawa da aka bawa Rara, ta kira taron da taron bogi

WhatsApp Image 2025 09 20 at 17.28.15 1 750x430

Jami’ar European-American University (EAU) ta karyata rahotannin da ke cewa ta ba mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, digiri na girmamawa a wani taro a Abuja.

A cikin sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, jami’ar ta bayyana cewa taron da aka ce an yi a NICON Luxury Hotel, Abuja, ya kasance ne ba bisa ka’ida ba, ba tare da sani ko amincewar jami’ar ba.

Jami’ar ta ce Rarara da wasu da aka ambata — Alhaji Ahmed Saleh Jnr., Prof. Mustapha Abdullahi Bujawa, da Prof. Tarela Boroh — ba su samu wannan digiri ba, kuma ba su da alaƙa da jami’ar.

Haka zalika, jami’ar ta ce Musari Audu Isyaku ba shi da hurumin wakiltar jami’ar, sannan kuma Idris Aliyu ba memba na kwamitin gudanarwa na jami’ar ba, kuma an soke nadinsa na Fellowship saboda hannu a wannan aikin bogi.

Jami’ar ta tabbatar da cewa tsohuwar mataimakiyar shugaban jami’ar, Dr. Josephine Egbuta, ba ta da hurumin wakiltar jami’ar, yayin da shugaban yanzu shi ne Professor Luca Scotto di Tella de’ Douglas di Castel di Ripa.

EAU ta ce za ta hada kai da hukumomin Najeriya don dakile fitar da takardun bogi da masu aikata laifin za a gurfanar da su.

Haka kuma, ta sanar da cewa taron girmamawa na hukuma a Najeriya zai gudana ranar 15 ga Nuwamba, 2025, sannan wani taro zai gudana a Malaysia a watan Disamba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here