Gwamnatin tarayya ta fara bincike kan wata cuta mai cin naman jiki a Adamawa

Adamawa map

Gwamnatin Tarayya ta fara bincike a dakin gwaje-gwaje domin gano musabbabin wata cuta mai cin naman jiki da ta kashe mutane bakwai a kauyen Malabu na jihar Adamawa.

Mukaddashin Kwamishinan shirye-shiryen kula da cututtukan Tarin Fuka, Buruli Ulcer da Kuturta na kasa, Dakta Adesigbin Olufemi, ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.

Olufemi ya ce zuwa ranar 10 ga Satumba, an tabbatar da mutane 67 da suka kamu da cutar, inda takwas daga cikinsu ke samun kulawar tiyata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama (MAUTH) dake Yola.

Ya ce wadannan tiyata na gudana da goyon bayan gwamnati don dakile gaggawar barkewar cutar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa cutar na fara bayyana ne a matsayin ƙurji, daga bisani sai ta fashe, ta rika cin naman jiki har ta kai ga illata ƙashi a wuraren da ta kama.

Ko da yake ba a tabbatar da asalin cutar ba, Olufemi ya bayyana cewa ana zargin Buruli Ulcer ce, cuta da wani ƙwayar cuta mai suna Mycobacterium ulcerans ke jawowa, wadda ake samunta a wuraren da ruwa ke tsayawa ko a cikin rafukan da ke da tabki.

Ya ce har yanzu ba a tabbatar da hanyar yaduwarta ba, duk da cewa wasu ra’ayoyi na nuna cewa kwari irin su sauro ko kwari masu zama a ruwa na iya shigar da cutar ga mutane lokacin da suka cije su.

Ya kuma yaba da yadda gwamnatin jihar Adamawa tare da hukumar tarayya da kungiyoyin agaji irin su REDAID suka dauki matakan gaggawa tun daga ranar 14 ga Satumba.

Olufemi ya kara da cewa wadanda ke da alamun cutar a matakin farko suna samun kulawa a cibiyoyin lafiya na yankin, yayin da wadanda cutar ta tsananta aka tura su manyan asibitoci domin yin tiyata.

Ya ce wayar da kan jama’a na da matukar muhimmanci domin a farko wasu mazauna yankin sun danganta cutar da sihiri, abin da ya jinkirta neman magani a asibiti.

A cewarsa, kauyen Malabu na da nisan awa biyu daga Yola, kuma hanyoyin shiga sun daure, abin da ke kara kawo cikas ga saurin kai dauki.

Ya jaddada cewa dorewar tsaron lafiya a yankunan karkara ba wai magani kawai ake bukata ba, har ma da samar da tsaftataccen ruwa da ingantaccen muhalli domin kauce wa dogaro da rafukan ruwa.

Ya tabbatar da cewa gwamnati tare da hadin gwiwar abokan hulɗa na kiwon lafiya na ci gaba da jajircewa wajen magance cutar da kuma dakile yaduwarta.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana Buruli Ulcer a matsayin daya daga cikin cututtukan da ake fi yi watsi da su a duniya, musamman a yankunan karkara da ke kusa da koguna wadanda basu da wadataccen kulawar lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here