Idan ina so na yi wa’adi na uku, da zan samu — Cewar Obasanjo

Olusegun Obasanjo new 750x430

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta zargin da aka dade ana yi masa cewa ya nemi tsawaita wa’adinsa fiye da biyu, yana mai cewa bai taba yin hakan ba.

Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin taron tattaunawar dimokuraɗiyya da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a birnin Accra.

Ya ce babu wani hujja da ke nuna cewa ya taba kiran wani ya fada masa cewa yana son wa’adi na uku.

“Idan ina so in samu wa’adi na uku, na san yadda zan yi”.

Babu wani ɗan Najeriya, ko mai rai ko mamaci, da zai ce na kira shi na gaya masa cewa ina so na yi wa’adi na uku.

Tsohon shugaban ya yi karin bayani cewa, samun rangwamen bashi ga Najeriya a lokacin mulkinsa abu ne mafi wuya fiye da neman tsawaita mulki.

Ya ce idan ya iya cimma hakan, babu shakka zai iya samun wa’adi na uku idan da shi yake nema.

Ya kuma gargadi shugabanni kan yiwuwar rike mulki da kyar, yana mai cewa hakan alamar ɗaukar kai a matsayin dole ne ga ƙasa, alhali kuwa babu wanda ya zama wajibi.

“Ina yawan gaya musu cewa mafi kyawun aiki ana yi ne yayin da mutum ke da kuzari da hangen nesa, amma wasu sun dauka cewa idan ba su nan, babu wani da zai iya.

Wannan laifi ne a gaban Allah, domin idan Allah ya ɗauki ran mutum, wani zai zo, kuma watakila zai yi daidai ko kuma ya fi shi,” in ji shi.

Obasanjo ya jaddada cewa shugabanni su daina jin cewa sai su ne kadai za su iya ciyar da kasa gaba, domin lokaci na kowa yana da iyaka.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here