Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya reshen Kano NBA ta bayyana takaici kan abin da ta kira maimaituwar cin zarafi da kuma kamun lauyoyi ba bisa ka’ida ba daga jami’an ’yan sanda a jihar.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Usman Umar Fari, ya rattaba hannu a kai ranar Talata, kungiyar ta kawo misalai guda biyu na baya-bayan nan da ta ce sun sabawa haƙƙin bil’adama tare da nuna barazana ga aikin lauya.
A cewar kungiyar, a ranar 19 ga Satumba, 2025, wasu jami’an ’yan sanda daga Abuja sun cafke lauya mai suna Mohammad Bashir Adam a lokacin da yake gudanar da aikinsa.
Duk da ya nuna katin shaidarsa ta kungiyar da kuma wurin aikinsa, an ce an daura masa ankwa aka kuma ja shi a gaban abokan huldarsa cikin mota zuwa Abuja, kafin daga baya a sake shi bayan jami’an sun gane kuskuren tantancewa.
Haka kuma, a ranar 22 ga Satumba, 2025, kungiyar ta ce jami’an Cibiyar Kasa ta Yaki da Laifukan Intanet ta rundunar ’yan sanda sun kama wani lauya, Uba Sani Hamza, a kotun majistare ta Norman’s Land da ke Kano. An tafi da shi Abuja bisa zargin suna daya da wani da ake nema saboda zagin jami’an gwamnati a dandalin sada zumunta da kuma kasancewarsa da wani abokin huldarsa da ’yan sanda ke nema.
Kungiyar ta bayyana wadannan lamurra a matsayin abin takaici da ke nuna keta haƙƙin ɗan adam a karkashin jagorancin Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa.
Ta kuma bukaci babban lauyan gwamnati ya shiga tsakani domin tabbatar da adalci tare da tabbatar da saki nan take ga Hamza.
Kungiyar ta dora alhakin tsaron lafiyarsa da jin dadinsa a kan gwamnatin tarayya.
Fari ya jaddada cewa kungiyar za ta ci gaba da kare haƙƙin lauyoyi da kuma tabbatar da mulkin doka a Najeriya.













































