Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta sake kama kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, kan zargin almundahana, jaridar Premium Times ta rahoto.
Mun dai ji cewa a ranar Alhamis da ta gabata, jami’an hukumar sun kama Mista Oluomo a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagas.
Sai dai kuma, an saki kakakin majalisar a daren ranar Juma’a sannan aka nemi ya dawo ofishin hukumar a ranar Litinin.
A lokacin da kakakin majalisar ya koma ofishin na EFCC a ranar Litinin, sai aka tsare shi.
Wata majiya ta ce Mista Oluomo da wasu mutane biyu da ake zargi suna tsare a hannun EFCC har zuwa karfe 9:43 na dare. Rahoton ya kuma ce daga kakakin majalisar har hadiminsa, Abdulgafar Adeleye, basu amsa kiran waya ba balle a ji ta bakinsu kan lamarin.













































