Na samu duk goyon bayan da nake bukata a masana’antar Kannywood – Prince Daniel Aboki

WhatsApp Image 2025 03 25 at 17.04.25

Daraktan shirin fim ɗin Mai martaba Prince Daniel Aboki ya sanar da cewa, bai yi hira da wata jarida ko kafar yada labarai ba dangane da cewa masana’antar Kannywood ta ki amincewa da shi saboda addininsa, ita kuma Nollywood saboda shi dan Arewa ne, kamar yadda ake ta yadawa a baya-baya nan.

A cewarsa, ya halarci wani taron masana’antar Nollywood da Hollywood a birnin Los Angeles na jihar California dake kasar Amurka a farkon wannan watan, inda a sashen tambaya da amsa na taron aka tambaye shi ƙalubalen da suka fuskanta lokacin yin Fim din Mai Martaba da gwagwarmayar kaiwa matakin kambun fina-finai na duniya na Oscars.

Ko da ya tashi bada amsa sai ya ce “Na ambaci batutuwa da dama irin su fargabar matsalar rashin tsaro yayin yin Fim tare da ma’aikata masu yawa a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da matsalolin kudi wanda babu wanda yake son yin kasadar amincewa ya bamu kudinsa la’akari da cewa ni sabon darakta ne wanda ke aiki tare da rukunin sababbin jarumai”.

“A wani lokacin bangaren masana’antar Kannywood na yi mana kallon ‘yan Nollywood, su ma Nollywood suna kallonmu a matsayin ‘yan Kannywood, saboda kawai ni dan Arewa ne”. In ji Aboki.

Karanta: Matan Kannywood nada bukatar a basu dama wajan shirya fina-finai – Shugabar kungiyar K-WAN

Ya ce, ya yi wannan bayanin ne da kyakkyawar niyya domin taimaka wa masu sauraro a cikin zauren su fahimci ɓangarorin masana’antar Fina-finai a Najeriya da kuma yadda yake da ƙalubale, sai dai an yiwa wannan bayanai nasa gurguwar fahimta.

“Domin fayyace zahiri, masana’antar Kannywood ba ta taba nuna min kiyayya ba ta kabilanci ko addini ba, hasalima, masanba’antar itace babban ginshiƙin goyon bayan da na samu a matsayina na mai shirya fim”. A cewar daraktan.

Aboki ya kuma ce, an nuna masa kauna a fili ta hanyar babban goyon bayan da ya samu daga masu kallo da sauran al-umma a lokacin da ya fara nuna fina-finan sa a gidajen kallo, da kuma karfafawa daga kwararrun ‘yan masana’antar tsofaffi da sababbin shiga.

“A yau ina alfahari, ni dan Film ne a Najeriya, wanda na fito daga arewa. Ina zaune a jihar Kano, inda nake gudanar da sana’ar tawa, daga Kannywood, kuma na samu goyon baya mai yawa, ba tare da nuna bambanci ba.

Saboda haka na tsaya tsayin daka wajen hada kai da takwarorina da wadanda suka kafa masana’antar Kannywood domin daukaka martabar masana’antarmu da bayar da labaranmu ga duniya da samar da guraben aikin yi ga matasanmu, tare da fito da zahirin halin da muke ciki sabanin labaran da ake bayarwa akan Arewa da ke nuna rikici da matsalolin rashin tsaro”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here