Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Merino ya taimakawa kungiyar sa wajen warware kwallon da Chelsia ta sanya musu a wasan hamayya na birnin London da aka buga inda aka tashi da ci 1-1.
Chelsia dai ta kare wasan da yan wasa 10 sakamakon samun jan kati na kora da dan wasan ya Moises Cacedo ya samu kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Canjaras din da kungiyar Arsenal din ta yi da Chelsia ya sa ta ci gaba da zama a matsayin ta daya a teburin gasar firimiyar Ingila da maki 30.
Hakan ya sa ya baiwa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City tasar mako biyarz wadda take a matsayin ta biyu da maki 25.
Sai kuma Chelsia da suka yi wanan da ita game a matsayin ta uku da maki 24.













































