U-20 AFCON: Najeriya ta doke kasar Egypt tare da lashe kyautar Tagulla

Flying Eagles

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Matasa yan kasa da shekaru 20 Flying Eagles sun doke kasar Egypt a bugun daga kai sai mai tsaran raga da ci 4-1 a gasar cin Kofin Afrika da ake bugawa yanzu haka a kasar ta Egypt.

An fafata wasan ne a ranar Lahadi 18 ga watan Mayun shekarar 2025.

Kafin yin bugun daga kai sai mai tsaran ragar dai an tashi a wasan Flying Eagles na dai ci 1 yayin da Egypt itama ke da ci 1.

Wannan nasarar ce ta sanya Najeriya ta lashe kyautar Tagulla karo na biyar kenan a tarihin ta na gasar.

Za dai a fafata wasan neman gurbin na uku a ranar 30 ga watan Yuni mai kamawa a filin wasa na Cairo dake kasar.

Kasar Egypt dai ta shiga gaban Najeriya mintuna 3 da fara wasan ta hannun dan wasa Osama Omar bayan da ya karbe kwallon daga hannun Mahmoud Labib.

Flying Eagles dai ta warware kwallonta mintuna biyu bayan dawowa daga hutum rabin lokaci inda dan wasa Bidemi Amole a mintuna na 47.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here