Jami’an tsaro sun cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Yahaya Zango a sansanin alhazai na Abuja a lokacin da ake gudanar da aikin tantance shi tare da wasu alhazan da ake shirin jigilar su zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wata majiyar tsaro a sansanin da ta tabbatar da kamun a ranar Lahadi, ta ce Zango wanda ya fito daga Paikon-Kore a karamar hukumar Gwagwalada a birnin tarayya Abuja, ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zarginsa da hannu a wasu jerin garkuwa da mutane.
“Da yammacin yau ne a lokacin da ake gudanar da tantancewar a sansanin Hajjin da ke filin jirgin sama, sai jami’an DSS suka kama shi suka tafi da shi,” majiyar ta ce an kama shi ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen jigilar alhazai.
Zango ya gabatar da fasfo dinsa na kasa da kasa tare da shiga jerin gwano tare da wasu mahajjata kafin jami’an DSS suka gano shi tare da kama shi.
Karin karatu: Hukumar DSS ta kama masu garkuwa da mutane da suka kashe wanda suka sace a Kano
Da yake tabbatar da kamun, wani babban jami’in Hukumar Jin Dadin Alhazai ta FCT, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar cewa wanda ake zargin ya yi gudun hijira kuma an kama shi a daidai lokacin da aka fara aikin tantance mutanen.
Har yanzu dai hukumar ta DSS ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan kamen ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.













































