Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wasu mutane 5 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka kashe wata yarinya ‘yar shekara daya mai suna Sakina Mamuda a kauyen Dhun Bake da ke karamar hukumar Gwarzo.
SolaceBase ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun hada da Zailani Rabiu, Hafizu Yusuf, Abubakar Abdulkareem, Umar Lawan da Amadu Salisu, dukkansu ‘yan unguwa daya ne, tare da wadda aka kashe a karamar hukumar Gwarzo.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa kokarin hukumar ta DSS kan matakin da ta dauka cikin gaggawa na cafke wadanda ake zargin.
Sanarwar ta ce wadanda ake zargin sun yi garkuwa da jaririyar ne kuma suka bukaci iyalanta da su biya kudin fansa, bayan sun yi mata kisan gilla.
“Duk da haka, wadanda suka aikata laifin sun jefar da gawar ta cikin wata tsohuwar rijiya,” in ji sanarwar.
Karin karatu: Gwamnan Kano ya biya diyyar sama da Naira miliyan 640 ga wadanda aikin kawar da zaizayar ƙasa ya shafa
Ya ce a halin yanzu ana binciken su da laifin hada baki, garkuwa da mutane, da kuma kisan kai.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai na hadin guiwa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Kano, Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Isa Dederi, tare da Kwamishinan Yada Labarai da sauran manyan jami’ai, sun jaddada aniyar gwamnati na ganin an tabbatar da adalci cikin gaggawa da kuma taka tsantsan a cikin wannan mummunan lamari.
Gwamna Yusuf ya nuna matukar alhininsa da faruwar lamarin, ya kuma yabawa jami’an DSS da sauran jami’an tsaro da suka dauki matakin da ya dace.
Ya kuma kara jaddada aniyar gwamnatinsa na karfafa jami’an tsaro na jihar ta hanyar kara zuba jari a fannin tattara bayanan sirri, dabaru, da hadin gwiwar hukumomi.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa duk wani jami’in tsaro da kayan aiki da kayayyakin da ake bukata don yakar miyagun laifuka, yayin da ya yi kira ga ‘yan kasa da su kasance masu lura da kuma tallafa wa kokarin jami’an tsaro ta hanyar musayar bayanai kan lokaci.
Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda ake kira da a gurfanar da wadanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba, sannan kuma a gurfanar da duk wani mai cutar da yara kanana.