Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa majalisar dattawa wasika yana neman ta tabbatar da nadin mutane 19 a matsayin shugaba, Manajan Darakta da mambobin hukumar gudanarwar (NCDC).
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasikar Tinubu yayin zaman taron na ranar Alhamis.
Wasikar tana cewa: Tinubu ya nemi hakan “Bisa ga tanadin sashe na daya, sashe na 2(2)(a) na dokar hukumar raya arewa ta tsakiya (da aka samar) a 2024.
Wadanda aka naɗa “Su ne Shugaba Cosmas Akyhir, Benue, Tsenyil Yiltsen, Manajan Darakta; Plateau, Dauda Kigbu, Memba; Nasarawa, Zakari Jikantoro, Memba; Niger.
Karin karatu: Hukumar DSS ta kama masu garkuwa da mutane da suka kashe wanda suka sace a Kano
Sauran su ne Sulaiman Ali, memba; Kogi, Rev. Bunmi Olusona, mamba; Kwara, Dr Umar Mantu, memba; Plateau, Atotse Abraham, memba; Benue
“Solomon Adodo, memba; Abuja, Abdulkadir Usman, memba; Arewa maso Gabas, Habu Mamman, memba; Arewa maso gabas Dr Atinuke Owolabi, memba; Kudu-maso-Yamma.
“Racheal Nse, memba; Kudu-South, Boniface Izziogu, memba; Kudu-maso-Gabas, James Uloko Babban Daraktan, Benue, Atika Ajanah, Babban Darakta, Ayyuka; Kogi.
“Hajiya Bilgis Sanni daraktan zartarwa, Kwara, Hajiya Aishatu Ibrahim Daraktar zartarwa Nasarawa da Muhammad Bashar Daraktan zartarwa Niger.(NAN)