Gwamnatin tarayya ta ce ta rage kudin sufuri ga ‘yan Najeriya da kashi 50 cikin 100.
Ministan ma’adinai, Dele Alake, ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja kan harkokin sufurin jama’a musamman a lokacin bikin kirsimeti.
Alake ya ce za a fara shirin ne daga ranar Alhamis, 21 ga Disamba, a karkare a ranar 4 ga Janairun 2024.
“Wannan dalili ne ya sanya gwamnatin tarayya sanar da cewa tun daga ranar Alhamis za a rage kudin sufuri a fadin Najeriya.
“Abin da hakan ke nufi shi ne, ‘yan Nijeriya masu son yin balaguro za su iya shiga motocin Safa a kan rangwamen kashi 50 na farashin da ake biya a halin yanzu”.
Masu hawa jiragen kasa suma yanzu zasu iya hawa cikin sauki a wannan lokacin na hutun kirsimeti.”
Karanta wannan: An rantsar da Simon Lalong a matsayin Sanata
Ya kara da cewa, shugaba Bola Tinubu ya amince da hakan bisa nuna soyayyar sa ga ‘yan Najeriya.
A cewarsa, matakin zai baiwa ‘yan Najeriya da ke son yin balaguro da ‘yan uwansu zuwa garuruwansu damar yin hakan ba tare da fargaba ba.
Alake ya bayyana cewa, Tinubu ya umarci ‘yan sanda da jami’an farin kaya DSS da sojoji da sauran jami’an tsaro da su hada kai don ganin an gudanar da bukukuwan lafiya a kasar nan.
“Yayin da muke yi wa daukacin ‘yan Nijeriya fatan alheri, muna rokon kowa da kowa ya kasance mai bin doka da oda, ya kasance mai kula da tsaro, mu zama masu kula da ‘yan uwanmu da iyalai da abokanmu da kuma makwabta”. in ji shi.












































