An rantsar da Simon Lalong a matsayin Sanata

Simon Lalong
Simon Lalong

An rantsar da Simon Lalong a matsayin Sanata mai wakiltar Filato ta kudu, kuma tuni ya maye gurbin Sanata Napoleon Bali.

Kotun daukaka kara ce dai ta soke nasarar zaben da Sanata Napoleon Bali ya samu a zaben na watan Fabrairu.

An rantsar da Sanatan ne a farkon zaman majalisar na ranar Laraba, a wani takaitaccen biki da akawun majalisar ya shirya.

Karanta wannan: Manyan Hafsoshin Sojoji 113 Sun Yi Ritaya

Sabon Sanatan wanda lauya ne kuma shugaban majalisar dokokin jihar Plateau wa’adi biyu, ya rike mukamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi na gwamnatin shugaba Tinubu.

Lalong ya mika takardar murabus dinsa ne ga shugaban kasar a kebe bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi a ranar Larabar da ta gabata.

Idan za a iya tunawa, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, a ranar 7 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da cewa Sanata Lalong, ne ya lashe zaben.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here