Jimillar hafsoshin sojojin Najeriya 113 a ranar Talata suka yi ritaya.
Hakan na dauke cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig. Gen. Onyema Nwachukwu ya fitar.
A cewar sanarwar, wadanda sukai ritayar sun hada da Janar daya, Laftanar Janar daya, Manjo Janar 67, da Birgediya Janar 44.
Sanarwar ta ce, Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya bukaci sojojin da su ci gaba da yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar da kuma goyon bayan ci gaban dimokradiyya a kasar.
A wajen bikin liyafar cin abincin da aka shirya domin karrama sabbin manyan hafsoshin sojojin Najeriya da suka yi ritaya a Abuja, Badaru, ya yaba da goyon bayan da sojojin Najeriya ke ba su wajen bunkasa dimokradiyya a kasar.
Badaru ya ce hakan ya sanya rundunar ta zama abin koyi a yankin Afirka ta Yamma da ragowar kasashe, inda ya bukaci sauran jami’an sojin da su zagi dantse dan ganin an ciyar da Najeriya gaba.