‘Yan majalisar dokokin jihar Rivers su 25 sun fara zama a Fatakwal babban birnin jihar.
‘Yan majalisar karkashin jagorancin Martin Amaewhule sun yi taro a harabar majalisar.
Sanarwar janyewar na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun mutane 27, da Martins Amaewhule ya karanta.
Ko da yake daya daga cikinsu yana kwance a asibiti kuma bai halarci taron ba.
Amaewhule ya ce hakan ya yi dai-dai da matakin kwamitin sasanta rikicin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kafa.
Karanta wannan: An rantsar da Simon Lalong a matsayin Sanata
Jihar dai ta fada rikici ne sakamakon rashin jituwar da ta barke tsakanin Wike da gwamnan jihar Fubara.
A wani mataki na magance baraka, shugaba Bola Tinubu ya gana da bangarorin da ke rikici tare da tuntubar tsohon gwamnan jihar, Dakta Peter Odili.
Yanzu haka dai a iya cewa an yi sulhu a fadar Aso Villa da ke Abuja.
Rikicin da ke tsakanin Wike da Fubara ya raba kan ‘yan majalisar inda 27 daga cikinsu suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.
Jam’iyyar da a karkashin mulkinta Wike ke rike da mukamin ministan birnin tarayya a halin yanzu.