Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta kwace gidaje 14, filaye 25 da kuma gonaki uku da ake zargin kuɗin haram ne aka mallake su a yankin Arewa maso Yamma a Najeriya.
Hukumar ta ce a bangaren kudade kuwa, ta kwato Naira biliyan 7.269bn a Arewa maso Yamma, da Naira Miliyan 43.335 a Arewa maso Gabas, tare da Dala Miliyan 1.066 a Arewa maso Yamma.
Shugaban hukumar, Dr. Musa Adamu Aliyu ya bayyana haka ne a Kano yayin taron wayar da kan jama’a tare da ‘yan jarida daga yankin arewa maso yamma da Arewa maso Gabas.
Aliyu ya ce hukumar ta bibiyi ayyuka 1,440 da darajarsu ta kai Naira biliyan 271 inda aka gano ayyuka 767 a Arewa maso Gabas da 673 a Arewa maso Yamma.
Karin labari: ICPC za ta gurfanar da Farfesa Malumfashi da wasu mutane 2 a kotu bisa zargin almundahanar Biliyan 1
Ya jaddada cewa shigar da hannu daga jama’a da ‘yan jarida wajen bankado ayyukan da aka watsar shi ne ya tabbatar da cewa albarkatu sun kai ga jama’ar da aka nufa.
Shugaban ICPC ya bayyana cewa aikin hukumar yana da ginshiƙai uku: aiwatar da doka, rigakafi, da kuma wayar da kan jama’a.
Wannan ya yi daidai da sashe na 6 na dokar ICPC ta 2000.
Ya ce bincike ya nuna cewa Arewa maso Yamma ce ke da mafi girman kaso na kin karbar rashawa a kasa (76%), yayin da arewa maso gabas ta kai (60%).
Haka kuma, rahotannin bayar da cin hanci daga arewa sun karu daga kashi 4.7% a 2019 zuwa kashi 13.4% a 2023, inda yawan rahotannin da aka dauki mataki a kansu ya ninka sau uku.
Aliyu ya bukaci Majalisar dokoki ta tura doka gaba domin kare ‘yan kasa daga tsoron bayar da rahoto, tare da yin kira ga kafafen yada labarai da su tallafa wa yaki da cin hanci ta hanyar sahihan bincike da rahotanni masu gaskiya ba tare da tashe hankalin jama’a ba.













































