DSS ta gurfanar da Kwamandojin Ansaru a kotu bisa tuhumar fasa gidan yarin Kuje

Ansaru leaders 750x430

Hukumar tsaro ta DSS a ranar Alhamis ta gurfanar da manyan kwamandoji biyu na haramtacciyar kungiyar ta’addanci Ansaru a gaban kotun tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta’addanci.

Wadanda ake tuhumar su ne Mahmud Usman wanda aka fi sani da Abu Bara’a Abbas ko Mukhtar, da mataimakinsa Mahmud Al-Nigeri wanda ake kira Malam Mamuda.

Ana zarginsu da kitsa harin kurkukun Kuje a watan Yuli 2022 wanda ya haifar da guduwar fursunoni sama da 600, da kuma kai hari kan m sojojin Najeriya a Kainji, jihar Neja, a 2022.

DSS ta bayyana cewa sun samu horo kan makamai, dabarun yaki da kuma hada bama-bamai a sansanonin ta’addanci na Mali da Libya.

Mamuda an ce ya samu horo na musamman tsakanin 2013 zuwa 2015 a hannun malamai masu tasirin jihadi daga kasashen waje.

Kwamandojin sun kuma shiga cikin manyan masu garkuwa da mutane, ciki har da sace injiniyan Faransa, Francis Collomp, a 2013, da kuma Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, a 2019.

Labari mai alaƙa: Fasa gidan yarin Kuje: DSS ta gurfanar da shugabannin kungiyar Ansaru da laifukan ta’addanci

Haka kuma ana zarginsu da fashi da makami da shirin kai hari kan tashar ma’adinan uranium a Neja da aka hana cimma nasara.

Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya tabbatar da kama su a wani samamen hadin gwiwa, inda ya bayyana Usman a matsayin shugaba na Ansaru wanda ke jagorantar ta’addanci daban-daban a Najeriya, yayin da Mamuda ya kasance babban yaro sa da ke shugabantar tawagar Mahmudawa a kusa da Kainji National Park.

Ribadu ya ce wannan samame ya karya cibiyar shugabancin Ansaru tare da bude hanyar hallaka kungiyar baki daya.

Ansaru ta balle daga Boko Haram ne a 2012 a Kano, tana ikirarin cewa za ta kasance “kungiya mai tausayi”, sai dai daga bisani ta hada kai da kungiyoyin jihadi na duniya, har ta rungumi tambarin AQIM a matsayin alamar kawance.

A wani lamari mai nasaba da hakan, DSS ta kuma gurfanar da Huzaifa Haruna bisa zargin jigilar bindigogi M-16 guda bakwai daga kauyen Dogo a Barikin Ladi, jihar Filato, zuwa hannun wani Wakili Julde a Wase.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here