Lagos: ’Yan sanda sun kama tsohon ɗan fursuna bisa zargin satar kayan ado na Zinare a Allen Avenue

5EE 750x430

Yan sandan jihar Legas sun cafke wani mutum mai suna John Samuel, mai shekaru 28, wanda ake zargin ɗan fashi da makami ne kuma ɗan haya a kashe-kashe, bisa satar kayan ado da kuma harbin wani ɗan kasuwa mai suna Gbenga Obama.

A watan Agusta, an harbi Obama sannan aka kwace masa kayan ado a bainar jama’a a kan titin Gbajobi, Allen Avenue, Ikeja, inda ake zargin Samuel ne ya aikata laifin.

A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa an kama wanda ake zargi a maboyarsa da ke Epe ranar 19 ga Satumba da misalin ƙarfe 2 na rana.

Rundunar ta ce Samuel ya fito daga gidan yari kwanan nan amma ya sake komawa aikata laifi, inda ya kwace wa Obama sarƙar zinariya mai tsada da sauran kayayyaki.

“John Samuel tsohon ɗan fursuna ne da aka san shi da tsananin tayar da hankali wajen fashi da makami, kashe-kashe da kuma kisan wasu daga cikin waɗanda ya rutsa da su.

Ya fito daga gidan yari bayan shafe shekaru kan babban laifin fashi da makami,” in ji sanarwar.

Binciken CCTV ya nuna yadda Samuel ya harbi wanda ya kai wa hari da bindiga ƙurar pistol a ranar 18 ga watan Agusta kafin ya kwace masa sarƙar zinariya, yayin da abokin aikinsa ke jiran shi a kan babur don tserewa.

An bayyana cewa wanda abin ya faru da shi ya samu raunuka masu tsanani, amma an yi masa magani kuma an sallame shi daga asibiti.

Rundunar ’yan sandan ta ƙara da cewa Samuel ya amsa cewa ya sayar da kayan adon da ya sace a kan Naira miliyan huɗu, “ƙasa da ainihin kimar su.”

Ta kuma bayyana cewa tana ƙoƙarin cafke sauran ’yan kungiyar domin gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Legas, Olohundare Jimoh, ya gargadi masu aikata laifi da cewa “Legas ba ta da mafaka gare su,” tare da ƙarfafa mazauna birnin su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here