Jam’iyyar PDP Ta Yi Allah-wadai Da Cin Zarafin ‘Yan Jarida A Kwara

abdulrahman abdulrazaq
abdulrahman abdulrazaq

Jam’iyyar PDP ta yi Allah wadai da ci gaba da cin zarafi da tsare wasu ‘yan jarida biyu ta hanyar amfani da gwamnatin Kwara.

Jam’iyyar ta bayyana damuwarta kan tsare wasu ‘yan jarida biyu, Abdulrazaq Aiyelabegan Babatunde da Lukman Oluwatoyin Bolakale, wadanda ke buga jaridun Just Events Online da Satcom Media a kwanakin baya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na jihar Kwara, Olusegun Olusola Adewara (Sholyment) ya fitar a karshen mako.

‘’Abin takaici ne a ce a cikin al’ummar dimokuradiyya, ana cin zarafin ‘yan jarida.”

‘Yancin ‘yan jarida wani ginshiki ne na duk wani dimokuradiyya mai inganci, kuma dole ne a bar ‘yan jarida su gudanar da ayyukansu ba tare da fargabar ramuwar gayya ba,” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here