Abdullahi Ata ya taya shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje murnar karin wa’adin mulki

Ganduje Ganduje new 750x430

Karamin ministan gidaje da raya Birane, Alhaji Abdullahi Ata ya taya Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje murnar kara wa’adinsa har zuwa 2026.

An amince da matakin yayin taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairun 2025, a fadar shugaban kasa a Abuja, kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranta, inda ya nuna irin dacewar jam’iyyar ga shugabancin Dr. Ganduje, kamar yadda wata sanarwa da Seyi Olorunsola, mai taimaka wa karamin ministan gidaje da raya birane, ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce, tun bayan da Dr. Ganduje ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar na kasa a ranar 3 ga watan Agusta, 2023, ya nuna shugabanci na musamman, inda ya jagoranci jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zabuka daban-daban.

Sanarwar ta kara da cewa, ‘’A jihar Edo, dan takarar jam’iyyar APC, Sen. Monday Okpebolo, ya samu gagarumar nasara a zaben gwamna da aka yi a watan Satumbar 2024, lamarin da ke nuni da yadda jam’iyyar ke kara yin tasiri a yankin.

Hakazalika, a jihar Ondo, sake zaben gwamna Lucky Aiyedatiwa a watan Nuwamban 2024 ya kara tabbatar da rinjayen APC a yankin Kudu maso Yamma.

Karin labari: Na gaji bashin sama da Naira Biliyan 8.9 a ofishin shugaban jam’iyyar APC – Ganduje

Nasarar da jam’iyyar ta samu ya kai jihar Kogi, inda Usman Ododo ya yi nasara a zaben gwamna da aka yi a watan Nuwamba na 2023, da kuma jihar Imo, inda aka sake zaben gwamna Hope Uzodimma a karo na biyu.

Wadannan nasarorin zaben sun kara karfafa kudurin APC na samar da shugabanci nagari da kuma amincewar da masu zabe ke da shi ga manufar jam’iyyar na samun ci gaba mai dorewa.

Sanarwar ta ce, dimbin gogewar da Dakta Ganduje ya samu a fagen siyasa, wanda ya hada da shekaru takwas a matsayin Mataimakin Gwamna da kuma wasu shekaru takwas a matsayin Gwamnan Jihar Kano, ya taka rawa wajen karfafa tsarin jam’iyyar da kuma samar da hadin kai a tsakanin mambobinta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here