Kakakin Hukumar ‘Yan Sanda na Ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa ‘yan sanda na da ikon shiga duk wani gida ba tare da samin izini ba idan sun ga alamar an aikata laifi a wurin.
Ya fadi hakan ne yayin martani kan wani faifan bidiyo da ke yawo, inda aka nuna wasu ‘yan sanda masu sanye da riguna marasa kyau da sutturar rufe fuska sunawa kutsa wani gida.
Mutanen gidan sun ki bude ƙofar suna masu cewa ba za su bude wa mutane da suka rufe fuska ba tare da nuna katin shaida ko izini ba.
Daga bisani, ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya harba bindiga sannan ya tsallaka katanga ya shiga gidan.
Adejobi ya ce, duk da ikon da ‘yan sanda ke da shi na shiga wuraren da ake zargin an aikata laifi, rufe fuska da sanya riguna marasa kyau bai dace ba.
Ya ce an fara bincike kan lamarin domin gano ‘yan sandan da ke cikin bidiyon.
Hukumar ta yi alkawarin daukar matakin da ya dace kan lamarin, tare da tabbatar da bin doka da kare haƙƙin jama’a.












































