Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take.
Solacebase ta tattaro cewa dokar hana fita ta biyo bayan zargin kashe mutane 15 da kuma kona gidaje da dama da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kashe mutane 15 mazauna Agban Kagoro a karamar hukumar Kaura, a daren Lahadi.
A cewar wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a ranar Litinin, an yi hakan ne domin taimakawa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankunan, da ceto rayuka da dukiyoyi da kuma ba da damar maido da doka da oda.
Ya ce hukumomin tsaro na da cikakken izinin aiwatar da dokar hana fita.
Gwamnati ta yi kira ga daukacin al’ummar kananan hukumomin Jema’a da Kaura da su ba jami’an tsaro hadin kai a wannan aikin na gaggawa na maido da zaman lafiya da bin doka da oda.
Gwamnati ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula da duk wasu ayyukan ta’addanci da suka afku a yankin.













































