Na gaji bashin sama da Naira Biliyan 8.9 a ofishin shugaban jam’iyyar APC – Ganduje

Ganduje

Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa ya gaji bashin kudaden Shari’a da suka kai Naira biliyan 8.98, wadanda suka samo asali daga shari’o’in gabanin zabe, shari’o’in zabe, da kararrakin da suka shafi zabukan ‘yan majalisa, gwamna, da na shugaban kasa.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka gudanar a gidan Buhari da ke sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a Abuja.

A cewarsa, mashawarcin jam’iyyar na kasa kan harkokin shari’a ya yi bakin kokarinsa wajen ganin an rage nauyin basussuka ta hanyar tattaunawa da wasu hanyoyin warware takaddamar, amma har yanzu wasu daga cikin asusun jam’iyyar na ci gaba da yin garambawul saboda wasu ɓangarori na shari’a.

Karin karatu: Zargin almundahana: Kotu ta sanya ranar da za ta saurari shari’ar Ganduje da matarsa da wasu 6.

Ganduje, wanda ya kuma yi magana kan nasarorin da ya samu a cikin shekara daya da rabi da yayi, ya jaddada cewa a halin yanzu shugabancin jam’iyyar ya mayar da hankali ne wajen lashe zabukan gwamna da za a yi a jihohin Anambra da Osun.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya bayyana yadda ake kokarin sasantawa a cikin jam’iyyar, inda ya bayyana cewa tuni aka fara samun sakamako mai kyau.

Taron na NEC ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka hada da gwamnonin Edo, Benue, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Niger, Lagos, Kogi, Ogun, Imo, da mataimakin gwamnan Ebonyi da tsoffin gwamnonin Kogi, Kebbi, Niger, Zamfara, Plateau.

Sai dai fitattun wadanda suka halarci taron sun hada da: Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

A yayin da jam’iyyar APC ke shirin gudanar da zabuka masu zuwa, shugabannin jam’iyyar na ci gaba da fuskantar rigingimun cikin gida, kalubalen shari’a, da kuma salon siyasa domin tabbatar da matsayin ta kafin 2025.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here