Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya watsi kan jita-jitar da ake yadawa na zargin mutuwarsa ta hanyar yada hoton bidiyonsa yana aikace aikace a dakin motsa jiki.
Tinubu a karshen mako ya sanya wani hoto me motsi da tsawon dakika 8 da aka nuno sa yana motsa jiki awani guri da ba a bayyana ba.
Martanin Tinubu na zuwa ne adaidai lokacin aketa rade-radin rashin lafiyarsa ce ta sanya rashin halartar rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun siyasa suka yi a makon jiya.
Tinubu a shafin nasa na sada zumunta da ya wallafa mai taken: “Da yawa sun ce na mutu; wasu kuma na cewa na janye daga yakin neman zaben shugaban kasar baki daya. To… a’a kalau nake.
“Wannan ita ce gaskiyar batu: Ina da ƙarfi da kuzari na, kuma ina cikin koshin lafiya a shirye nake nayi aiki tukuru da sauke nauyin ga alumma ‘yan Najeriya tun daga rana ta ɗaya idan na lashe zabe.”
Da yawa sun ce na mutu; wasu kuma na cewa na janye daga yakin neman zaben shugaban kasa.
Tun da farko, Daraktan yada labarai da yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Tinubu na cikin koshin lafiya a birnin Landan na kasar Birtaniya.













































