Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke wasu ‘yan baranda da ake zargin an dauka hayar su domin kawo cikas a zaben cike gurbi da aka gudanarwa a karamar hukumar Kunchi ta jihar.
Usaini Gumel, kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, a ranar Asabar.
Gumel wanda bai bayyana adadin mutanen da aka kama ba ya ce barayin da aka kama suna da makamai.
Ya ce ana zargin wani dan siyasa ne da ke takara a zaben ya dauki hayar su.