Majalisar ƙoli ta shari’a ta yi Allah-wadai da kashe-kashen Jos, ta bukaci gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa

supreme council for sharia

Majalisar koli ta shari’a a Najeriya SCSN ta yi Allah-wadai da kashe-kashen fararen hula da suka faru a Angwan Rukuba da ke Jos, tana bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba.

A cikin wata sanarwa da sakataren janar nata, Nafiu Baba Ahmad, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, majalisar ta nuna matukar bacin rai kan harin tare da bukatar hukumomi su wuce matakin fitar da sanarwar Allah-wadai kawai, su dauki kwakkwaran mataki domin dakile tashin hankalin.

Majalisar ta bayyana cewa yadda ake yawan samun hare-hare sannan a rika mayar da martani da kalaman Allah-wadai kawai ya zama abin damuwa, tana mai jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyi shi ne babban nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati a kowane mataki.

Ta kuma jaddada cewa addinin Musulunci yana mutunta rayuwar dan Adam ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, tare da gargadin cewa kashe mutum ba bisa ka’ida ba babban laifi ne a bangaren addini da kuma dabi’a.

Majalisar ta bayyana harin Angwan Rukuba a matsayin wanda ake zargin an shirya shi tun da wuri domin tayar da rikicin addini da na al’umma a yankin da tuni yake cikin mawuyacin hali.

Haka kuma ta nuna damuwa kan yiwuwar shigar wasu kungiyoyi masu karfi da kudi ciki har da na kasashen waje, wajen rura wutar tashin hankali ta hanyar yada makamai da tallafa wa kungiyoyin ta’addanci.

Majalisar ta bukaci gwamnati ta gano tare da daukar matakin da ya dace kan masu daukar nauyin tashin hankalin daga waje da kuma masu hadin kai na cikin gida ta hanyar amfani da bayanan sirri da hadin gwiwar yankuna.

Ta kuma nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a wasu sassan arewacin Najeriya musamman yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma, inda al’umma ke fuskantar matsalolin ta’addanci, fashi da makami da kashe-kashe.

Majalisar ta mika ta’aziyya ga gwamnatin jihar Plateau da al’ummar ta da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tana addu’ar samun sauki da juriya a wannan lokaci mai wuya.

Ta kuma bukaci shugabannin addinai su rika karfafa zaman lafiya, hakuri da fahimtar juna a tsakanin mabiyansu, tare da kira ga ‘yan kasa su yi magana kan duk wanda ke haddasa rikici.

Majalisar ta kuma nemi a gudanar da cikakken bincike cikin gaskiya da adalci kan lamarin, tana mai cewa dole ne hukumomin tsaro su yi aikinsu yadda ya kamata domin ganin an yi adalci.

Ta bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu bin doka, masu lura da kuma hadin kai domin fuskantar duk wani yunƙuri na raba kan kasa, tana gargadin cewa kasar ba za ta iya ci gaba da tafiya a wannan tafarki na tashin hankali ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here