Hare-haren Jos: Gwamnatin tarayya za ta girke kyamarorin CCTV 5000 a Plateau domin sa ido – Tinubu

IMG 20260402 WA0042 533x400 1

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce mafita mafi dacewa ita ce Jos ta koma yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka santa da shi a baya.

Ya jaddada cewa babu yawan jimami da zai iya dawo da waɗanda aka rasa, yana mai tunatar da cewa an zaɓi shugabanni ne domin samar da zaman lafiya da walwala, ba wai ƙara yawan zawarawa da marayu ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ziyararsa zuwa Plateau State, inda ya kai ziyara sakamakon hare-haren baya-bayan nan da suka yi sanadin mutuwar mutane 28 tare da jikkata wasu da dama.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa zuwansa ba don jajanta wa kaɗai ba ne, har ma don inganta zaman lafiya mai ɗorewa, yana mai cewa irin waɗannan hare-hare bai kamata su sake faruwa ba.

Ya umurci dukkan shugabannin tsaro da su gano tare da gurfanar da waɗanda suka aikata hare-haren da suka faru a jihar Plateau.

Tinubu ya kuma tabbatar da cewa za a girke sama da kyamarorin CCTV 5,000 domin ƙarfafa tsarin sa ido kan tsaro a fadin jihar.

A nasa bangaren, Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital, Bosun Tijani, ya ce za a girke kyamarorin sa ido a dukkan jihohin ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na inganta tsaro da hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here