Jam’iyyar APC ta ce matakin hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC na soke amincewa da ɓangaren jam’iyyar ADC da David Mark ke jagoranta ya yi daidai da hukuncin kotu.
Sakataren yaɗa labarai na APC na ƙasa, Felix Morka, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, yana mai mayar da martani kan lamarin.
Ya ce matakin INEC na soke amincewa da shugabannin ɓangaren ADC da David Mark ke jagoranta ya yi daidai da hukuncin kotu kuma yana da inganci a doka.
Ya ƙara da cewa matakin ya dace kuma ya yi daidai da manufofin zaɓe da tsarin dimokuraɗiyya, yana mai cewa hakan sakamakon kuskuren da jam’iyyar ta jefa kanta ciki ne.
Morka ya ce ADC na ƙoƙarin kauce wa alhaki ta hanyar dora laifi kan APC kan matsalolin cikin gida da ita ce ta haddasa.
Ya kuma zargi ADC da zama taron ‘yan siyasa masu son zuciya tare da yada ra’ayoyin ƙage a kan APC.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ADC tun farko ba ta da ƙarfi, kuma an gina ta ne da tsarin da zai jawo rushewar kanta cikin sauƙi.
Haka kuma ya zargi shugabancin ɓangarori karkashin David Mark da Rauf Aregbesola da kwace jam’iyyar ta hanyar karya kundin tsarin mulki.
Ya ce gazawar ADC wajen tafiyar da harkokinta na cikin gida ya sa ba ta cancanci zama jam’iyyar da za a ɗauka da muhimmanci ba a idon ‘yan Najeriya.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar da ba za ta iya gyara kanta ba, ba za ta iya gyara ƙasa ba.
A cewarsa, ADC ba ta da wani abin bayarwa face sukar APC kawai.
Ya kuma tabbatar da cewa APC da shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da aiwatar da shirin “Renewed Hope Agenda” domin ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da samar da zaman lafiya da ci gaba a ƙasar.
NAN













































