
Ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, a ranar Lahadin da ta gabata ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi umarnin fara aikin gina babbar hanyar da ta tashi daga Sakkwato zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1000 nan take.
Umahi ya yi magana bayan ya duba karshen sashe na daya, mataki na daya, na babbar hanyar Legas zuwa Kalaba da kuma yadda aka daidaita ta a Lagos.
“Na yi farin ciki da cewa shugaban kasa ya kuma umurce ni da in fara zanen babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagry.
Karin labari: “Karancin Man fetur zai dauki a kalla makonni biyu” – IPMAN
“Wannan ita ce babbar hanya da ta ke da kilomita 1000.
“Mun fara zayyana kuma ina da tabbacin da zarar Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shi, za mu fara ne daga bangaren Sakkwato, wanda shi ne ma’auni.
Har ila yau, muna da wani yunkuri wanda zai tashi daga Enugu – Abakaliki-Ogoja zuwa Kamaru.
“Don haka muna da wannan karfin kuma yana da nisan kilomita 361, mu bi ta Otukpo zuwa Benue zuwa Nasarawa kuma ya kare a Apo a Abuja.
Karin labari: SSCE: Gwamnatin Jigawa ta amince da fiye da Naira Miliyan 23 ga daliban Sakandire
“Za mu kuma gabatar da shi ga shugaban kasa, kuma idan aka yi haka, to, hanyoyin bakin teku kamar yadda muka yi alkawari za su zagaya kasar baki daya,” in ji shi.
Ministan ya ce bayan kammala aikin titin da ke bakin tekun zai hade yankunan Kudu-maso-Yamma da Kudu-maso-Kudu da Arewa-maso-Gabas da kuma Arewa-maso-Yamma tare da Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Umahi ya bayyana kokari da jajircewarsa kan muhimmancin aikin titin bakin teku, wanda ya ce zai zama na farko a Afirka.












































