An yi arangama tsakanin jami’an ‘yan sandan Senegal da masu zanga-zangar adawa

soji, zanga-zanga, senegal, 'yansanda
Jami’an tsaro a Senegal sun kame guda cikin jagororin adawar kasar Aminata Toure da ta jagoranci zanga-zangar adawa da dage lokacin gudanar da babban zaben...

Jami’an tsaro a Senegal sun kame guda cikin jagororin adawar kasar Aminata Toure da ta jagoranci zanga-zangar adawa da dage lokacin gudanar da babban zaben kasar, gangamin da ya juye zuwa arangama tsakanin masu boren da ‘yan sanda.

A ranar Asabar din da ta gabata ne, shugaba Macky Sall na Senegal ya sanar da dage lokacin gudanar da zaben kasar wanda aka tsara bisa ka’ida zai gudana a ranar 25 ga watan nan, ba kuma tare da sanar da tsayayyen lokacin gudanar da shi ba.

Karanta wannan: Rundunar ‘yan sandan Kano, ta cafke ‘yan daba da ke kokarin kai hari wuraren da ake zaben cike gurbi a jihar

Tuni dai matakin ya haddasa tarnaki a sassan Senegal wanda ya kai ga zanga-zangar bangaren adawar yayinda kungiyar tarayyar Turai ta bayyana matakin a matsayin rashin tabbas game da yiwuwar iya gudanar da zaben na Senegal, a bangare guda Amurka ta nemi lallai shugaba Macky Sally a gaggautar tsayar da lokacin gudanar da zaben.

Dubban mutane ne daga dukkan matakai suka tsunduma zanga-zangar a jiya Lahadi wanda jami’an ‘yan sanda suka rika harba hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa dandazon baya ga kame wasu daruruwa ciki har da tsohuwar Firaministar kasar Aminata Toure da ta yi shura wajen kakkausar suka ga shugaba Sall.

Karanta wannan: INEC Ta Dakatar Da Zaɓe A Jihohi 3 Saboda Tarzoma

A wani jawabin kai tsaye ta gidan talabijin ne Macky Sall ya sanar da matakin tare da rushe dokar zaben da ta haddasa cece-kuce bayan fitar da sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaben na bana ba tare da wasu daga cikinsu ba.

A cewar Macky Sall a sanya hannu kan wata sabuwar doka wadda za ta yi karan tsaye ga yarjejeniyar watan Nuwamban bara da ta kai tsayar da ranar gudanar da zaben sai dai ba tare da shugaban ya bayar da wata sabuwar ranar yin zaben ba.

A watan jiya ne hukumar kundin tsarin mulkin Senegal ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaben ba tare da sunan wasu ‘yan takarar jam’iyyun adawa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here