Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Lateef Fagbemi, ya ce babu wata doka a Najeriya da ta haramta gurfanar da yara kanana.
Fagbemi ya bayyana haka ne a Abuja ranar Juma’a yayin da yake zantawa da ‘yan jarida dangane da umurnin da kotu ta bayar na sakin kanan yaran da sukai zanga-zanga, guda 114 wadanda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar da su a baya.