Gobara ta kone shaguna 20 a kasuwar Ibadan

gobara, kone, shaguna, 'yan katako, jihar, kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta kone kantuna 21 a kasuwar 'yan katako da ke Rijiyar Lemo a karamar hukumar Dala a Kano...

Wata gobara da ta tashi cikin dare ta yi sanadin konewar shaguna sama da 20 tare da lalata dukiyar miliyoyin kudi a kasuwar Sango-Oju Irin da ke Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa a Jihar Oyo, gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki a kasuwar.

Aminiya ta rawaito cewa, wannan shi ne karo na uku da gobara ke tashi a birnin, tun bayan shigowar sabuwar shekara.

A baya-bayannan gobara ta tashi har kashi biyu a sassan birnin daban-daban, lamarin da ya kai ga asarar dukiya mai tarin yawa.

Kansila mai wakiltar Ibadan ta Arewa, Oluwayemisi Adeagbo, ya tabbatar da cewa ba’a rasa rayuka ba.

Karanta wannan: An yi arangama tsakanin jami’an ‘yan sandan Senegal da masu zanga-zangar adawa

“Gobarar ta faru ne a sakamakon matsalar wutar lantarki. Yawancin ‘yan kasuwar da abin ya shafa sun riga sun tashi. Jama’armu da yawa bashi suka ci don kara jari duba da yadda hauhawar farashin kayayyaki ke karuwa kullum.

“Muna kira ga gwamnati da ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su taimaka domin kada asarar da aka yi ta haifar da matsala ga wadanda abin ya shafa,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here