Masu kiwon kaji sun koka da asarar Naira Tiriliyan 3 kan tabarbarewar Tattalin Arziki

Masu Kiwon, Kaji, Asara, Tattalin Arziki
Masu kiwon kaji a fadin kasar nan sun ce mambobinsu sun yi asarar sama da Naira Tiriliyan 3 a jarin da suka yi a halin da ake ciki a shekarar 2023 a kasar...

Masu kiwon kaji a fadin kasar nan sun ce mambobinsu sun yi asarar sama da Naira Tiriliyan 3 a jarin da suka yi a halin da ake ciki a shekarar 2023 a kasar nan.

Masu kiwon karkashin kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya PAN reshen jihar Legas, sun bayyana haka yayin da suke zantawa da NAN ranar Litinin a Legas.

Shugaban kungiyar PAN reshen jihar Legas, Mista Mojeed Iyiola, ya ce halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya ya tilastawa yawancin mambobinta barin sana’ar.

Karanta wannan: Gobara ta kone shaguna 20 a kasuwar Ibadan

Iyoha ya ce kungiyar ta yi asarar makudan kudaden shiga a shekarar 2023, biyo bayan rufe wuraren kiwon kaji da akasarin mambobin kungiyar suka yi, wadanda suka kasa cika bukatunsu na kudi don ci gaba da kasuwancinsu.

A cewarsa, tasirin da aka yi na rufe wuraren kiwon kaji mai yawa a kasar nan a fannin tattalin arziki mai girman gaske ne tun daga shekarar 2023.

“Tun bayan rufe kusan kashi 50 na gonakin kaji a fadin kasar nan, fannin ya yi asarar sama da Naira tiriliyan uku.

“Wannan shi ne saboda a kowace jiha a kalla muna asarar Naira biliyan 6, muna so mu ci gaba da jan hankalin mambobinmu da kada su bar sana’ar duk da matsalolin da ake fuskanta,” in ji Iyiola.

Karanta wannan: Rundunar ‘yan sandan Kano, ta cafke ‘yan daba da ke kokarin kai hari wuraren da ake zaben cike gurbi a jihar

Wani tsohon shugaban kungiyar PAN reshen jihar Legas, Mista Lanre Bello, ya bayyana cewa rufe irin wadannan wuraren kiwon kaji ya haifar da asarar ayyukan yi da kuma cin basussuka daga mambobin kungiyar.

“Tasirin tattalin arzikin da aka yi na rufe wuraren kiwon kaji a fadin kasar nan yana da yawa.

“Daya shi ne dimbin asarar ayyukan yi da aka yi a fannin, mutane da dama kuma sun yi asarar jarin da suka zuba, kuma a yanzu sun ci bashi saboda rashin iya biyan basussukan da suka karba.

“A zahiri ba za’a iya ƙididdige illolin da aka yi asara ba kuma hanya ɗaya da za’a gyara ita ce a kai agaji ga manoman kaji, dole ne mu ba da taimako ga fannin saboda kaji ya kasance tushen furotin mai inganci kaji da kwai ba zan ce suna da arha ba amma suna da araha,” in ji Bello.

Karanta wannan: Gwamnatin Jigawa zata Kashe biliyan 1.4 domin gyaran Makabartu da  Masallatai

Ya kuma sake jaddada muhimmancin kayan kiwon kaji ga abincin ɗan adam, musamman yara.

“Masu kula da abinci mai gina jiki sun ce kwai na samar da fiye da kashi 50 cikin 100 na abubuwan da ake bukata na furotin a cikin abincin ɗan adam da kuma taimakawa ci gaban kwakwalwa ga yara.

“A yawancin abincinmu, furotin yana ɓacewa kuma idan muka bar shi ya ci gaba, za mu fuskanci matsala mafi haɗari.

“Wataƙila za mu fara samun raguwar girma a cikin yara, wanda al’amarin da muka fara shaidawa,” in ji shi.

NAN ta rawaito cewa a yanzu ana siyar da kwandon kwai tsakanin Naira 3,200 zuwa 3,500 gwargwadon girmansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here