Sheikh Daurawa ya zama babban limamin Masallacin juma’ar da Kwankwaso ya ginawa mahaifinsa

IMG 20221023 WA0324 720x430 1
IMG 20221023 WA0324 720x430 1

Babban malamin addinin musulincin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya zama babban limamin masallacin juma’ar da sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ginawa mahaifinsa.

Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da gidauniyar kwamkwasiya ta fitar mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa da kuma Dakta Yusuf Ibrahim Kofar mata.

An nada Daurawa a matsayin babban limamin masallacin tare da wasu manyan malama a matsayin na’ibai a masallacin dake miller road, a unguwar Bompai dake karamar hukumar Nasarawa Kano.

Dan takarar shugabancin kasar a Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ginawa mahaifinsa Alhaji Musa Kwankwaso, wanda ya rasu a 24 ga watan Disamba, na shekarar 2020.
Sauran limaman massallacin sun hada da Sheikh Sadiq Isa Abdullahi, Sheikh Gwani Baffa Ite, Sheikh Bazallah Nasir Kabara da kuma Malam Ashir Nata’ala.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here