2023: Dan majalisar wakilai ya fice daga APC zuwa PDP

IMG 20221023 WA0003
IMG 20221023 WA0003

Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar mazabar Ageui/Lapai a majalisar wakilai Hon Ibrahim Ebbo ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Hon Ibrahim Ebbo wanda kuma wakili ne a kwamitin yakin neman zaben Tinubu ya mika wasikar yin murabus dinsa ga shugaban jam’iyyar APC na gundumar mazabar sa ta Ebbo/ Gbacneli.

Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar tarayya ya yi alkawarin yiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar aiki a lokacin zabukan 2023.

Idan za a iya tunawa shugaban kasa Muhammad Buhari aranar juma’a ne ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a dakin taro na Banquet Hall dake Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here