Kwastam za ta rabawa jama’a kayan abincin da ta kwace

kwastam, raba, kayan abinci, jama'a
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana shirinta na raba kayan abinci da ta kama ga ’yan kasar domin rage wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu...

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana shirinta na raba kayan abinci da ta kama ga ’yan kasar domin rage wahalhalun da suke fuskanta a halin yanzu.

Hukumar ta ce za’a yi rabo kayan abincin ne bayan an tantance su an tabbatar da cewa ba su da hadari ga lafiyar dan Adam.

Dubban ’yan Najeriya dai sun gudanar da zanga-zanga a kan tituna kan halin kunci da tsadar kayan masarufi a kasar.

Karin labari: Kamfanonin siminti sun amince rage farashin siminti

Kan haka ne shugaban hukumar ta NCS, Bashir Adewale Adeniyi ya bayyana shirinsu a ranar Talata, na raba kayan abincin da aka kama ga ’yan Najeriya

Kakakin Hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada ya sanar cewa daukar matakin ya dace da aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na wadata kasa da abinci.

Karin labari: Akpabio ya fallasa gwamnoni da karbar Naira Biliyan 30

A cewarsa, matakin na gaggawa ne kuma daukar sa na da muhimmanci wajen samun wadatar abinci a Najeriya da kuma dakile illar karancinsa ga ’yan kasa.

“Za’a sanar da hanyoyin da za’a bi wajen rabon kayan ta ofishin hukumar a duk fadin Najeriya, domin tabbatar da adalci da tabbatar da cewa amfanin ya isa ga wadanda suka fi bukata,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here