Amurka tace akwai alamun kaddamar da kai hare hare a Abuja

DSS sabo
DSS sabo

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya ce akwai alamun fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci a Najeriya musamman a babban birnin tarayya Abuja.

A cikin wata sanarwar da Ofishin ya raba wa ‘yan kasarta, Ofishin Jakadancin Amurka ya ce harin ka iya shafar ‘yan kasa da wadan da ba yan kasar ba, kuma ba’a iyakance shi ga, gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, manyan kantuna, otal-otal, mashaya, gidajen cin abinci, wuraren wasannin motsa jiki, tashoshin sufuri da sauran gurare.

“Ofishin jakadancin Amurka zai tsaya da kaddamar wasu ayyuka har sai an samu wata sanarwa,” in ji ofishin jakadancin Amurka.

Ofishin jakadancin Amurka ya shawarci ‘yan kasar da su guji duk wani tafiye-tafiye ko tsayawa agurare ma su cunkoson jama’a tareda kai rahotanni ga hukuma mafi kusa da zarar basu gane wani abu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here