‘Yan daba sun cinna wa Ofishin hukumar zabe wuta a Ebonyi

Burnt INEC Office in Ebonyi 750x430 1
Burnt INEC Office in Ebonyi 750x430 1

A karshen mako ne wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta da ke karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kakakin hukumar zabe kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, a ranar Lahadi.

Wannan dai shi ne hari na uku da aka kai kan ofisoshin kananan hukumomin zabe cikin makonni uku, bayan hare-haren da aka kai a jihohin Ogun da Osun.

Lamarin da ya faru da misalin karfe 10 na safe wanda ya haddasa kone duk wani abu na cikin Ofishin.

A cewar sanarwar, abubuwan da suka kone sun hada da akwatunan zabe 340, kambun zabe 130, injinan wutar lantarki 14, manyan tankunan ajiya na ruwa, da kayayyakin ofis iri-iri da na’urori da kayan aiki da har yanzu ba a tantance adadin katunan zabe na dindindin ba dasuka kone.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here