Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta ceto wata mata mai suna Hadiza Chado mai shekaru 20 da haihuwa daga gidan masu garkuwa da mutane tare da kama wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a cikin lamarin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Tafida ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Dutse ranar Alhamis.
Tafida ya ce an yi garkuwa da ita ne ne a ranar 8 ga watan Janairu a kauyen Marma da ke karamar hukumar Kirikasamma ta jihar.
Ya ce an kubutar da wadda abin ya rutsa da ita ne a ranar Laraba, bayan da ‘yan sanda suka kai samame a maboyar wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Suletankarkar.
Ya ce ‘yan sandan sun kuma kai samame maboyar ‘yan ta’adda guda uku a kauyukan Dajin Maizuwo, Dan Gwanki da Yandamo da ke yankin a yayin farmakin.
“Bindigu AK-47 guda uku, mujallu tara da rayayyun alburusai gudda 308, bindigu aka kama a yayin samamen.
“Mun kuma kwato motar bas Toyota Hummer guda daya, babura tara, wayoyin hannu guda shida, katin SIM 12, da katin ajiya guda biyar,” in ji shi.
CP ya kara da cewa an kuma kwato Naira miliyan 2.7 yayin aikin.
Ya ce, biyu daga cikin bindigu da aka kwato an tafi da su daga hannun jami’an ‘yan sanda da aka kashe a lokacin da suke amsa kiran gaggawa a ranar 23 ga watan Janairu a kauyen Kwalam da ke karamar hukumar Taura.
Tafida ya ci gaba da cewa daya daga cikin baburan da aka gano na daya ne mai suna Abdu Sajo, kwamandan jami’an tsaro da aka kashe a ranar 25 ga watan Janairu.
A cewarsa, za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
Ya nanata kudurin ‘yan sanda na yaki da miyagun laifuka da kare rayuka da dukiyoyi a jihar.













































