Jirgin farko na kamfanin jiragen sama na Najeriya Air, mallakin Gwamnatin Tarayya, wanda ta dade tana alkawarin zai fara aiki, yana hanyarsa ta zuwa Abuja daga kasar waje.
Aminiya ta gano cewa a safiyar Juma’a jirgin Nigeria Air ya fara lodi daga Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha zuwa Abuja, Babban Birnin Tarayya, kwana uku kafin saukar gwamnatin Shugaba Buhari da ta kafa kamfanin.
’Yan Najeriya dai sun sha cewa sun gaji da gafara sa, ba su ga kaho ba, sakamakon alkawuran da gwamnatin ta sha yi na fara aikin jiragen Nigeria Air ba tare da hakan ya tabbata ba.
A yayin da gwamnatin Buhari ke shirin nade tabarmarta, Ministan Sufuri, Hadi Sirika, wanda ministan ya dauki gabarar kafa kamfanin, ya yi alkawarin jiragen za su fara tashi kafin gwamnatin ta mika mulki.
Sai dai tun a farkon shirin ya yi ta cikin karo da matsaloli da kuma adawa daga masu ruwa da tsaki, da ke ganin hakan ko dai barnar kudi ne, ko kuma ba a tsara shi yadda ya kamata ba.
(Aminiya)













































