Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, ya ce, Najeriya na ci gaba da gudanar da aikin bututun iskar Gas na dala biliyan 25 da nufin tura iskar Gas din zuwa kasashen Turai ta gabar tekun yammacin Afirka.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin ganawa da kungiyar Vitol Group, babbar dillalan kayayyaki masu zaman kansu inda suka gana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa bututun iskar gas daga Najeriya zuwa Morocco zai kai iskar Gas dinne daga Najeriya zuwa Marocco, sannan ya wuce zuwa nahiyar Turai.
Shettima ya ce, shugabancin Bola Tinubu ya bayar da dama ta musamman ga masu zuba hannun jari na duniya, musamman tare da manyan gyare-gyaren da za su sake fasalin tattalin arzikin Najeriya.
Haka kuma ya lura da kwazon gyare-gyaren da Tinubu ya yi ya sanya Nijeriya a matsayin wata kyakkyawar cibiyar zuba jari, musamman a fannin makamashi da ababen more rayuwa.
Ya kuma yi kira ga masu zuba jari da su amince da sabuwar alkiblar tattalin arziki karkashin Tinubu.













































