Hukumomi a Sifaniya sun ce sun gano wasu mutane uku da suka makale a bindin jirgin ruwa, bayan shafe kwana 11 a kan hanya daga Najeriya.

Wani hoto da dakarun bakin teku suka wallafa ya nuna mutanen zaune a wani bangare na injin jirgin, yayin da kafafunsu ke lilo.

An kai mutanen uku asibitin garin da jirgin ya tsaya, Gran Canaria, domin duba lafiyarsu.
Babu tabbas ko suna zaune a kan bindin ne a tsawon tafiyar.
Bayanai daga shafin da ke bibiyar sufurin jirgen ruwa ya nuna cewa katafaren jirgin ruwan dakon kayan ya isa Gran Canaria na Las Palmas ne daga birnin Legas na Najeriya – inda ya yi tafiyar mil 2,700.












































