Daraktan kula da lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar Nangere ta jihar Yobe, Malam Ibrahim Lawan, wanda a baya aka dakatar bisa zargin karkatar da sinadaran da ke ƙunshe da abubuwan gina jiki da aka samar domin Yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, ya amsa zargin da ake yi masa.
Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa, tun da farko hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Jihar ce ta dakatar da Lawan, sakamakon tuhumarsa da karkatar da sinadaran da ke gina jiki waɗanda aka samar domin Yara masu matsalar Tamowa.
Mista Adamu Abba, mai magana da yawun hukumar, wanda ya sanar da dakatarwar a ranar Laraba a Damaturu, ya ce an kafa wani kwamiti mai mutane biyar da zai binciki lamarin.
Lawan, yayin da yake mayar da martani kan zargin a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce shi da wasu ma’aikatan PHC “da gaske sun yi ta’ammali da kayan abinci na magani.