Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce an kashe mutane biyu tare da kona gidaje uku a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma a karamar hukumar Brinin Kudu ranar Talata.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da DSP Lawan Shiisu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) ya fitar a Dutse ranar Laraba.
Shiisu ya ce lamarin ya faru ne bayan wasu da ake zargin makiyaya ne daga jihar Katsina da ake zargin makiyayan sun gayyace su ne suka mamaye gonaki a kauyukan Safa da Gaurakai da ke yankin.













































