Mai Martaba Sarkin Ilorin kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadana na shekarar 2022 cikin nasara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Sarkin, Abdulazeez Arowona, ya fitar ranar Lahadi a Ilorin.
Yace za a gudanar da Sallar Idi ne Ranar Litinin 2 ga watan Mayu da misalin karfe 9 na safe a filin Sallar Idi na wanda babban Limamin Ilorin, Dakta Muhammad Bashir Imam-Soliu zai jagoranta.
A cewarsa, Sarkin ya gode wa malaman addinin Musulunci bisa jajircewar da suka yi wajen karfafawa mabiya gwiwa kan su kasance masu himma da yin addu’a kamar yadda Alkur’ani mai girma da Sunnah ke kunshe dasu.
Ya kara da cewa, jim kadan bayan kammala Sallar Idi, Sarkin zai karbi bakuncin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq da sauran manyan baki wadanda za su yi addua a fadarsa nan take kuma ya koma gida.
“Kazalika Sarkin ya yi kira ga al’ummar Masarautar Ilorin da su yi bukukuwan Sallah cikin nutsuwa da kuma kyautata al’ada tare da bayar da agaji da afuwa a lokacin bikukuwan Sallar da kuma bayan bikin.
“Ya kuma umarci matasa da su guji duk wani abu da zai iya kawo Tazgaro ga zaman lafiya a jihar inda ya bukace su da su bawa jami’an tsaro hadin kai wajen gudanar da ayyukansu” in ji Arowona.













































