Gwamna Zulum ya amince da nadin mukaddashin shugaban jami’ar Borno

Zulum, mukaddashi, shugaban, jami'a, borno, maiduguri, toro
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Farfesa Haruna Dantoro Dlakwa a matsayin mukaddashin shugaban jami'ar jihar Borno da ke...

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Farfesa Haruna Dantoro Dlakwa a matsayin mukaddashin shugaban jami’ar jihar Borno da ke Maiduguri.

SolaceBase ta rawaito cewa nadin Dlakwa na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Bukar Tijani ya fitar a ranar Laraba a Maiduguri.

Karin labari: Hukumar FAAN ta sake bude titin jirgin sama bayan hatsarin jirgin Dana

Sanarwar ta kara da cewa amincewar Zulum ya biyo bayan shawarar da majalisar gudanarwar jami’ar ta bayar bayan taronta na 10 da aka gudanar a ranar 15 ga watan Afrilu, 2024.

Farfesa Dlakwa ya kasance mataimakin shugaban jami’ar jihar Borno har zuwa wannan nadi.

Karin labari: Dangin wata amarya sun kashe dan ta’adda a jihar Zamfara

Sakataren ya ce, Gwamna Zulum ya mika sakon taya murna ga Farfesa Haruna Dantoro Dlakwa tare da fatan alheri.Farfesa Dan Toro

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here