Kanin Sanata Kwankwaso ya rasu

30A4A811 A43E 4A4F 89F1 76D712D8D0E4
30A4A811 A43E 4A4F 89F1 76D712D8D0E4

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rashin kaninsa, Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso, a safiyar yau Litinin.

Solacebase ta ruwaito cewa Inuwa Kwankwaso ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano yana da shekaru 64, bayan ya sha fama da jinya.

Wata sanarwa da shugaban Cibiyar yada labarai ta Kwankwasiyya, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce marigayin tsohon ma’aikacin gwamnati ne, kuma injiniyan aikin gona wanda ya samu horo a Ibadan da Amurka, kuma ya yi aiki da kamfanin shuke-shuken dazuzzuka a Kano tsawon shekaru.

Sanarwar ta kara da cewa Kwamared Inuwa Kwankwaso ya bar matarsa, ’ya’ya mata biyu Barr. Nafisa Inuwa da Zainab Inuwa da ‘yan uwa da dama.

A cewar sanarwar, za a yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a makabartar iyali da ke kauyen Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano da karfe 4:00 na yammacin yau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here