Wata budurwa mai shekara 20 ta kai mahaifinta kotu kan kokarin yi mata auren dole.
Matashiyar mai suna Fatima Aliyu daga garin Kaduna ta shaida wa kotun shari’ar Musulunci cewa tana da wanda take so, amma mahaifinta ke kokarin yi mata auren dole.
Mahaifin ya ce iyayensa kafin rasuwa ne suka zaɓa wa diyarsa mijin aure, shi ya sa yake kokarin cika alkawari.
Alkali Malam Aiyeku Abdulrahman, ya ce duk da yake mahaifi na da damar zaɓawa ‘yarsa mijin aure, a wannan gabar kokarin tilasta mata bai dace ba.
Ya shawarci mahaifin ya kara hakuri da diyar tasa.
Alkalin ya bukaci mahaifin ya bai wa ‘yarsa damar gabatar da mutumin da take so, sannan a yi bincike, idan babu wani laifi to a bar su su yi aurensu